Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Bidiyo

Shirin Inda Ranka 20-07-2022

Published

on

Magidanta da masana na cigaba da martani kan sanyawa masu adaidaita sahu takunkumin aiki idan har goman dare ta yi.

Wani matashi ya koka kan yadda budurwar da ya shafe shekaru biyu yana neman aurenta, bayan ta cinye masa shawarma da bankararrun kaji da wayoyin hannu sai wani let kwama ya yi wuff da ita.

Wata kotu anan Kano ta ce karamin sani kukumi ne, don haka ta aike da wani barawon tukunya zuwa hukumar HISBAH domin a koya masa Ahalari tun daga Auwalu Mayajibu har zuwa babin rabkannuwa a wajen Sallah.

Su kuwa ‘yan sanda sun cacume wata mata mai saurin fushi wace ta bankawa saurayinta wuta bayan da ta kama shi yana badala da wata mata.

Sai ku saurari shirin na Inda Ranka da Nasiru Salisu Zango ya gabatar domin jin cikakkun labaran.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!