Labarai
Shirin NEWMAP ya horas da manoma a Kano
Shirin kiyaye zaizayar kasa da kula da kananan madatsun ruwa NEWMAP, ya horas da manoman rani 50 daga kananan hukumomin jihar Kano 5 kan dabarun noman rani domin samar da ingantattu kuma wadataccen abinci a jihar Kano.
Da yake jawabi yayin karkare bada horon a yau Laraba, shugaban shirin a jihar Kano Malam Musa Shuaibu, ya bayyana cewa, an fara bayar da horon ne tun a watan disamban bara inda aka kammala shia a wannan wata na Yuni kuma an koyar da mahalarta horon sabbin hanyoyin da za su taimaka musu matika a harkar noma.
Haka kuma jamiin shirin na NEWMAP, ya kara da cewa yayin kammala horon a yau an raba wa manoman kyautar kayan aikin gonad a suka hadar da injin shuka da iri da maganin feshi da taki da sauran kayan aikin noma.
A nasa jawabin, kwamishinan maaikatar muhalli na jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso, ya bukaci manoman da su yi amfani da horo da kuma kayan aikin da aka basu yadda ya dace domin ciyar da kansu gaba.
Wasu daga cikin wadanda suka samu horon sun bayyana cewa, za su yi aiki da kayan da aka basu kamar yadda aka koya musu a taron horon.
Dr Kabiru Ibrahim Getso, ya kuma ja hankalin mahalarta taron da su rika daukar matakan kariya daga annobar COVID-19.
Bayan kammala boron dai an baiwa mutanen 50 shaidar kammalawa kamar yadda aka alkawarta musu.
You must be logged in to post a comment Login