Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu bayar da tallafin kayan noma ga manoman jihar kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce yanzu ta kammala shirin bayar da tallafin kayan noma ga al’umma jihar kano musamman a wannan lokaci da damina take daf da sauka domin samarwa da manoma saukin taki a wannan lokaci.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da safiyar yau yayin da ya karɓi baƙuncin sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero a fadar gwamnatin Kano cikin wani ɓangare na bikin sallah ƙarama.

Gwamna Yusuf ya kuma ce yanzu haka shirin samar da takin zamani da za’a bawa manoma yayi nisa domin samar da anfanin noma a kano.

Da yake jawabi tun da fari sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero kira yayi ga gwamnatoci da suyi duba da tunkarowar damuna wajen tallafawa manoma dake faɗin jihar nan dama ƙasa baki ɗaya.

Haka zalika gwamnatin kano tace zata tabbatar da cewa ta shiga lunguna da saƙo na jihar kano domin ganin ta tallafawa manoma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!