Labarai
Shirin samar da ayyukan yi ga matasa zai rage talauci a Najeriya – Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce ta bullo da shirin baiwa Matasa aikin yi na wucin gadi wato Extended special public work program a kasar nan don rage talauci, da yunwa da rashin aikin yi da sauransu.
Ministan tsaron kasar nan janar Bashir Salihi Magashi ne ya bayyana hakan yau ya yin kaddamar da shirin a nan Kano.
Ministan ya ce “manufar gwamnatin tarayya shi ne ta hanzarta baiwa matasan ‘yan Najeriya su 774000 aikin da koyar da su sana’o’i daga kananan hukumomi 774 na Najeriya”
A wani jawabi gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Nasir Yusif Gawuna ya yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan kokarin ganin cewa mutane 1,000 a kowace karamar hukuma zasu ci gajiyar Shirin tare da naira dubu 20 har zuwa wata uku.
Wakiliya Zahrau Nasir ta rawaito cewa hukumar samar da ayyuka ta kasa ce zata kula da yadda shirin zai rika gudana a kasar nan
You must be logged in to post a comment Login