Ƙetare
Shugaba Abdel Fattah al-Burhan ya yi watsi da kiran Amurka na tsagaita wuta

Shugaban mulkin sojin Sudan ya yi watsi da kiran da Amurka ta jagoranta na tsagaita wuta na wucin-gadi ta yadda za a ci gaba da tattaunawar kawo ƙarshen rikicina kasar ta sudan.
Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana shirin tsagaita wutar da ke samun goyon bayan Amurka da Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar a matsayin wata ajanda da ƙasashen wajen ke son ƙaƙaba wa mutanen Sudan.
Ya ƙara da cewa a shirye sojojin Sudan suke ga shirin zaman lafiya, idan har abokan faɗansu na rundunar RSF za su ajiye makamansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa mummunan faɗa a birnin El-Fasher da aka mamaye a arewacin Darfur, inda aka kashe dɗaruruwan fararen hula tare da raba dubbai da muhallansu.
You must be logged in to post a comment Login