Labarai
Shugaba Buhari ba zan baiwa ‘yan Najeriya kunya ba
Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya ce yana sane da nauyin da ke wuyan sa yana mai yin alkawarin cewa ba zai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba, wajen ganin ya tabbatar da kowanne dan kasar nan ya sami kyakyawar rayuwa.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a masalacin fadar gwamnati dake Abuja yayin da ake gabatar da tafsirin Alkur’ani mai girma da ake yi kullum a wannan wata na Ramadan mai alfarma.
Shugaban kasar ya kuma kara da cewar, nauyin da ke ofishin sa na cikin kokarinsa a koda yaushe, a don haka ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya sauke wannan nauyin da aka dora masa wajen ganin ‘yan Najeriya na rayuwa cikin kyakyawan yanayi.
A cewar Muhammadu Buhari ya san mai zai yi ga ‘yan Najeriya kuma ba zai taba basu kunya ba.
Shugaban kasar bai kammala jawabin sa ba, sai da ya gode wa ‘yan Najeriya bisa damar da suka bashi na sake shugabanci karo na 2, yana mai cewar zai cimma manufofin da ya sanya a gaba.
Da yake jawabi limamin masalacin fadar gwamnati Sheik Abdulwaheed Suleman yayi godiya ga Allah Saboda kammala zaben ban aba tare da samun tarzoma ba, yayin da kuma yayin addu’ar Allah ya kawo karshen kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.