Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya ce ‘yan Najeriya su yi watsi da kiran dattawan Arewa kan dawowar Fulani

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da kiran da kungiyar dattawan arewa ta yi al’ummar Fulani mazauna kudancin kasar nan na su bar yankin don dawowa arewa.

Muhammadu Buhari ya ce ko wane dan Najeriya yana da ‘yancin zama a duk inda ya yi muradi a fadin kasar, kuma babu wanda ya ke da ikon korar wani mutum ko wata kabila daga inda su ke.

Wannan jawabi na shugaban kasa na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai malam Garba Shehu ya fitar, yana mai ganin baiken kungiyar ta dattawan arewa da ma duk wata kungiya mai kokarin katsalandan kan al’amuran tsaron kasar nan.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta mayar da hankali sosai wajen ganin an kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a fadin kasar nan, ta hanyar samar da mafita guda da dukkannin bangarorin za su aminta da ita.

Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya su ba da ta su gudunmawar don ganin zaman lafiya ya inganta a kasar nan baki-daya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!