Labarai
Shugaba Buhari ya aike da ta’aziyyar sa ga kasar Ivory Coast
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ake da ta’azziyar sag a al’ummar kasar Ivory Coast bisa rasuwar firaministan kasar Amadou Gon Coulibaly wanda ake sa ran cewar zai tsaya takarar shugaban kasa a watan Okotoban da ya gabata.
Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafan yada labarai Garba Shehu ya sanar da hakan ta cikin sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa yace mutuwar Firaministan zai girgiza kasar kasancewar ya bada gudunmawa wajen ciyar da kasar ta Ivory Coast.
Ta cikin sanarwar Muhammad Buhari ya aike da ta’azziyar sag a shugaban kasar Alassane Ouattara da ma ilahirin gwamnatin kasa saboda firaministan ya rasu ne ya yin da yake sauke nauyin da aka rataya masa wajen cigaban kasar.
You must be logged in to post a comment Login