Labarai
Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaro su kara jajircewa akan aikin su
Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su kara jajircewa wajen tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dokiyoyin al’umma.
Muhammadu Buhari na wadannan kalaman ne lokacin da yake ganawa da manyan hafsojin tsaron a fadar Asorok da ke birnin tarayya Abuja.
Shugaban kasar ya kuma bukaci sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan da su yi kokari wajen dakile ayyukan ‘yan’ta’adda da masu garkuwa da mutane suna garkuwa da su.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da: Minstan tsaro Burgediya janar Mansur Dan Ali mai ritaya da babban hafsan tsaro Janar Abayomi Olonishekin , da babban hafsan sojin kasa Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, da kuma babban hafsan sojin ruwa Vice Admiral Ibok-Ete.
Sauran sun hada da: shugaban sashen bangaren tsare tsare na rundunar soji ta kasa Air Vice Marshal Emmanuel Achebi sai kuma mai rikon mukamin sufeto janar na ‘yan ’sandan kasar nan Muhammad Adamu.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ganawa da Shugaban kasa, Babban hafsan Sojin ruwa Vice Admiral Ibok-Ete, ya ce, ana samun raguwar adadin masu garkuwa da mutane a kasar nan, sai dai ya ce, yayin tattaunawar wasu daga cikin hafsoshin sun yiwa shugaban kasa bayani kan wasu sabbin hanyoyin da za’abi wajen kawo karshen matsalar yan’tadda a fadin kasar.