Labarai
Shugaba Buhari ya gana da shugabanin APC da wasu gwamnonin jam’iyyar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabanin jam’iyyar APC da kuma wasu gwamnonin jam’iyyar a dai-dai lokacin da mambobin ke kakar ficewa daga cikinta.
Dukkanin ganawar da shugaban kasar yayi an yi ne a fadar sa ta Aso Villa da ke birinin tarayya Abuja awanni kadab bayan da gwamanan jihar Sokoto Aminu Waziri Tanbuwal ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Haka zalika ganawa ta biyu an gudanar da ita ne da misalin karfe 9 45 na daren jiya da tsakanin shugaban kasar da wasu gwamanoni goma sha biya da mataimakin gwamna guda daya.
Haka zalika attorney Janar kuma ministan shari’a Abubakar Malami da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole sai kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha na daga cikin wadanda suka hakarci zaman.
Jim kadan bayan da aka kammala taro na farko ne aka jiyo shugan jam’iyyar APC Adams Oshiomhole na cewa ya zama dole shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki ya sauka daga kan mukamin sa na shugabancin majalisar tun da dai y bar jam’iyyar.
Oshiomhole, wanda ya gana da shugaban kasar tare da wasu sanatoci ya ce kujerar shugabancin majalisar ta na jam’iyar APC ne kawai don haka ya zama wajibi Saraki ya sauka daga kan kujerar.