Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya isa Legas domin kaddamar da matatar Dangote

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Birnin Legas domin kaddamar da sabuwar matatar man ta Dangote da aka gina a jihar, wadda ake sa ran za ta rika tace gangar mai dubu dari shida da hamsin a kowacce rana domin rage wahalar shigar da tataccen man Fetur a Nijeriya.

Ana saran wannan matata ta rika aikin tace man Fetur da man Dizal da Kalanzir da kuma man Jiragen sama.

Ana sa ran wannan matata za ta rage matsalolin da ake fuskanta a Nijeriya na rashin samun wadataccen man da ake tacewa a cikin gida.

Rahotonni sun bayyana cewa a makonni masu zuwa ake saran kamfanin ya fara aiki gadan-gadan a matatar wadda ita ce mafi girma da wani dan kasuwa ya mallaka a nahiyar Afrika.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!