Connect with us

Kiwon Lafiya

Jami’ar NOUN ta gargadi dalibai masu takarardun bogi

Published

on

Jami’ar Karatu daka gida ta ja hankalin dalibai da jami’an tsaro da sauran al’umma gaba daya kan takardun jarrabawar na bogi da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani da ke ake zargin daga hukumar makarantar suka fito.

 

Jami’in yada labaran Jami’ar ta NOUN Ibrahim Sheme ne ya bayyana haka a jiya Laraba a birnin tarayya Abuja.

 

Inda ya ce babu wata takardar jarrabawar da ta fito daga hukumar makarantar a hukuman ce ya kuma bukaci al’umma da su kaucewa batun.

 

Ya kuma ce jama’ar na iya kokarin ta wajen ganin ta girmama kanta da kare martabarta a idon duniya daga dukkanin irin wadannan abubuwan da ke faru da basu da tushe ballantana makama.

 

Sheme ya kara da cewa jami’ar ta NOUN ta shigar da korafi a rubuce ga hukumomin tsaro, inda ta bukaci  jami’an tsaron su bankado wanda ke da hannu kan wajen yada bayanan domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,742 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!