Labarai
shugaba Buhari ya mayar da daraktan hukumar kula da Inshorar lafiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da dakataccen shugaban hukumar kula da Inshorar Lafiya ta kasa Usman Yusuf bakin aiki.
Tun a cikin watan Yunin bara ne dai Ministan Lafiya Isaac Adewole ya dakatar da Usman Yusuf daga mukaminsa bayan kafa masa kwamitin bincike, sakamakon zarginsa da rashin da’a da badakala da kuma nuna fifiko ga wasu ma’aikata.
Isaac Adewole ya tabbatar da karbar wasikar bukatar mayar da Usman Yusuf bakin aiki sai dai bai yi karin hasken ko yaushe zai fara aikin ba kuma kan wane mataki.
Majalisar Dattijai ta a dawo da shugaban hukumar ta NHIS inda suka ce ba daidai bane Ministan ya dakatar da shi, har ma Usman Yusuf din ya ce ba zai amince da dakatarwar ba kasancewar ta saba da ka’ida.
Bayan fitar da bukaci sakamakon binciken da Kwamitin da Ministan Lafiyar ya kafa ya yi ne sai kuma Ministan ya aikewa dakataccen shugaban hukumar ta NHIS wasikar da ke nuni da cewa ya karbi rahoton mai dauke da kwanan watan 5 ga Oktoban bara, kuma ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin daukar mataki na gaba.