Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya nemi hadin kan takwaroin sa kan dawo da kudaden da aka sace

Published

on

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da takwarorin sa na kasashen Zambia da Ethiopia sun bukaci hadin kan Shugabannin Afirka wajen bukatar dawowa da nahiyar biliyoyin kudaden da aka sace aka boye a wasu sassa na duniya.

 

Shugaba Buhari da sauran takwarorin sa, na Afirka sun yi wannan jawabi ne a gefen taron majalisar dinkin duniya da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka.

 

Rahotanni sun ce ana zargin cewa duk shekara ana hada-hadar kudaden haramun da suka kai sama da dala biliyan hamsin a nahiyar afirka.

 

Da ya ke gabatar da jawabi shugaba Buhari, ya ce, Najeriya ta yi asarar sama da dala biliyan dari da hamsin da bakwai tsakanin shekarar dubu biyu da uku zuwa dubu biyu da goma sha biyu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!