Labarai
Shugaba Buhari ya tafi bikin rantsar da zababben shugaban kasar Senegal Macky Sall
Shugaban kasa Muhammadu na kan hanyar sa zuwa kasar Senegal don hallatar bikin rantsar da zababban shugaban kasar Senegal Macky Sall.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawon shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a dazu nan.
Sanarwar ta kara da cewar, Muhammadu Buhari ya amsa gayyatar da aka yi masa na hallatar bikin rantsuwar a matsayin sa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammancin Afrika EWOWAS, Zai zama babban bako a yayin bikin rantsuwar wanda shugabanin kasashen Afrika za su halarta da za’a yi a cibiyar nuna kayayyakin tarihi ta Diamniadio a gobe Talata.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu rakiyar Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa.
Sauran su ne ministan kasashen waje Mr Geoffrey Onyema da mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran tsaro Majo Janaral Babagana Monguno mai ritaya da babban darakta na hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Rufa’I da sauran kososhin gwamnati.
Ana saran cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya bayan kammala bikin rantsuwar a gobe Talata.