Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari ya tura wakili jihar Bauchi domin jajantawa kan ibtila’in da afku
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da wakilai karkashin jagorancin Ministan ilimi malam Adamu Adamu zuwa jihar Bauchi domin jajantawa kan ibtila’in guguwa da Ambali yar ruwan da ta afku a baya bayan nan a jihar Bauchi.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran fadar gwamnatin tarayya malam Garba Shehu ya fitar a jiya Talata.
Sanarwar ta ruwaito cewa akalla mutane takwas ne suka rasa rayukan su inda wasu 120 kuma suka samu raunuka sakamakon guguwa mai karfin da ta auku a jihar. Ka zalika kididdigar ta nuna sama da gida je 1000 ne suka salwanta.
Tawagar wadda har ila yau ta kunshi shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa Yunusa Mustapha Maihaja za ta duba irin asarar da aka yi yayin Ambaliyar ruwan da kuma asarar da aka yi a gobarar da aka yi a kasuwar Azare.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa hukumar ta NEMA ta fara raba kayan tallafin jin kai daga runbun adana kayayyakin ta da ke Damaturu jihar Yobe domin rabawa wadanda al’amarin ya shafa.