Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Guguwa ta kashe mutane 4 a jihohin Nassarawa da Taraba

Published

on

Wasu mutane uku sun rasa rayukansu a garin Takum da ke jihar Taraba sakamakon wata guguwa da ta faru sau biyu cikin kwanaki biyu.

BBC ta ruwaito wani mazaunin garin Mallam Maiwada Takum ya ce, guguwar ta soma faruwa ne da yammacin ranar Talata inda ta yi gagarumar ɓarna ga gidaje da makarantu da ofisoshi.

Ya ƙara da cewa da farko an yi mamakon ruwan sama daga bisani kuma aka yi guguwa mai ƙarfi da ta shafe fiye da sa’a ɗaya da rabi tana zagawa.

Shi ma wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya bayyana cewa guguwar ta yi matuƙar ɓarna inda ta salwantar da gidaje da rayuka.

Babban mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Emmanuel Bello ya ce gwamna Agbu Kefas ya higa garin domin duba irin ɓarnar da guguwar ta yi.

Haka kuma ta ruwaito cewa, an samu rahoton mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu da dama sakamakon tashin guguwa da ta lalata gidaje fiye da 100 a yankin Agbashi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nassarawa.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, John Bako-Ari ne ya tabbatar da lamarin inda ya ce guguwar ta tashi ne ranar Talata da yamma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!