Labarai
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren Sokoto
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da aka kai jihar Sokoto da kuma rikicin kabilanci da ya barke a jihar Kaduna.
Shugaba Buhari ya kuma yi gargadin cewa kisan wadanda basu ji ba basu gani ba, shakka babu duk wanda aka kama da hannu wajen aikata wannan danyen aiki zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban mataimakin sa na musamman kan al’amuran yada labarai Garba Shehu yau a Abuja.
A cewar shugaban Buhari kashe mutum daya, dai-dai yake da kasha mutane dari na al’ummar Najeriya , inda yace lokaci yayi da ya kamata ace masu aikata wannan danyen aiki an dauki tsauraran matakai a kan su.
Shugaban Buhari ya bayyana cewa masu aikata wannan danyen aiki be zamana ko yaushe ace suna samun nasara ba, saboda haka akwai yadda hukumomin tsaro zasu yi wajen cafko su a duk inda suke tare da gurfanar da su gaban shari’a.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma tabbatarwa da al’ummar Najeriya cewa basu cikakken tsaro shine abu mafi muhimmanci da gwamnantin sa ta sanya a gaba, inda yace ana cigaba da bawa jami’an tsaron kasar horon da ya kamata tare da samar da kayayyakin aiki a bangaren tsaro duk da nufin dakile kalubalen da ke addabar bangaren tsaro a fadin Najeriya.