Connect with us

Labarai

Yadda jirgin shalkwabta ya fado a Lagos

Published

on

Wani jirgin shalkwabta da ya fado a wani gini a jihar Lagos yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu wanda har yanzu ba a kai ga tantance ko su wanene ba.

Rahotannin sun bayyana cewa jirgin shalkwabtar mai dauke da fasinjoji uku ana kyautata zaton ya taso daga wata jihar ne inda kuma da misalin karfe 12 na ranar yau Juma’a ya yi hatsari.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos Olafemi Oke-Osanyintolu ne ya tabbatar da faruwar lamari, inda yace mutane biyu sun rasu nan take,

Ya yin da guda daya daga ciki aka mika shi zuwa sashin bada agajin gaggawa na asibitin koyarwa na jihar Lagos.

Olufemi ya kara da cewa, sun samu kiran gaggawa dake bayyana cewa wani shalkwabta ya fado kan wani gini a Ikeja dauke da mutane uku.

Yana mai cewa tuni hukumar su ta aike da gawarwakin mutanen zuwa bangare adana gawa na asibitin jihar Lagos yayin dayan ke karbar kulawa ta musamman.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!