Labarai
Shugaba Buhari zai kai ziyara Kasar Senegal
- Anasa ran yau Tallata Shugaban kasar Nijeriya zai Kai ziyara Kasar Senegal.
- Taron an shirya shine don bunkasa harkar Nima a nahiyar Afrika.
- Anasa ran taron ya taimaka wajen kawo karshen yunwar da ake fama da ita a kasashen Afrika.
A yau ne ake saran Shugaban kasar Nijeriya Muhammdu Buhari zai bar kasar nan zuwa kasar Senegal domin halartar taron kasa da kasa kan harkokin noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.
Mai magana da yawun shugaban kasar kan kafafen yada labarai Mista Femi Adesina ne ya bayyana hakan a jiya Litinin.
Taron Wanda shugaban Senegal kuma shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU, Macky Salla zai karbi bakuncin sa, an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma da zai ciyar da haniyar Afirka gaba.
Adesina ya ce ‘mahalrta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu kasashen, ciki har da Najeriya’.
Ya kara cewa ‘ ana sa ran taron ya kawo karshen yunwar da ake fama dashi a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030’.
Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.
Rahoto: Abdulkadir Yusuf Gwarzo
You must be logged in to post a comment Login