Labarai
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai jihar Benue
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a jihar Benue, inda aka kashe gomman mutane a yankin Umogidi da ke karamar hukumar Otukpo.
Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, yace shugaba Buhari ya yi kira da a dauki duk matakan da suka dace wajen ganin an dakatar da rikicin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito hukumomin tsaro a yankin da lamarin ya faru suna cewa, akalla mutum 74 aka kashe cikin makon da ya gabata a wasu hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka kai a jihar.
You must be logged in to post a comment Login