Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Muhammdu Buhari ya kai ziyarar aiki jihar Katsina

Published

on

Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Jihar Katsina domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Daga cikin ayyukan da shugaba Buhari zai kaddamar da budewa a yau Alhamis akwai Gadar kasa ta Kofar Kaura, da babban asibitin Katsina, da cibiyar nazarin harkokin da suka shafi yanayi wato Metrological Institute da dai sauransu.

Yayin da a gobe juma’a kuma zai kaddamar da bude babban asibitin garin Musawa, da hanyar Sandamu zuwa Baure zuwa Babban mutum zuwa Daura dama wasu da dama.

A daren jiya laraba ne dai shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa ‘Yar’adua, daga birnin Dakar na kasar Senegal, bayan halartar babban taron kasa da kasa na harkokin noma karo na biyu da aka gudanar.

 

Rahoto:Abdulkarim Muhammad Abdulkarim

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!