Labarai
Shugaba Tinubu ya ayyana 7 ga Afrilu a matsayin ranar Ƴan sanda
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sanda ta ƙasa.
Shugaba Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana hakan a daren ranar jiya Litinin yayin bikin karramawar da ‘yan sanda suka yi a otal ɗin Transcorp Hilton da ke birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana sake fasalin tunanin hukumomi da kuma tunawa da jami’an ‘yan sanda a matsayin wani muhimmin abu a yunkurin gwamnatinsa na mayar da rundunar zuwa cibiya ta zamani, kwararru da kuma rikon amana.
Ya ce gwamnatinsa ta bullo da sauye-sauye masu yawa domin farfado da rundunar ‘yan sandan kasar tun bayan hawansa ofishi a shekarar 2023.
Don haka ya jadadda bukatar shigar da maza da mata na rundunar wajen horas da su da kuma samar musu da kwararrun da ake bukata domin gudanar da aiki mai wahala na aikin ‘yan sanda na zamani.
You must be logged in to post a comment Login