Labarai
Shugaba Tinubu ya bada umarnin sassauta farashin kayan abinci

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci kwamitin harkokin noma na Majalisar Zartaswar Tarayya FEC da ya gaggauta daukar karin matakai domin kara rage farashin abinci a fadin kasar nan.
Ministan jihar harkokin noma da abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja, yayin wani taron horaswa na yini daya da aka shirya.
A cewar Sanata Sabi, gwamnatin tarayya na daukar matakan tabbatar da sahihin tsaro da saukin safarar kayan abinci daga gonaki zuwa kasuwanni, da nufin dakile hauhawar farashin kayayyakin abinci tare da saukaka wa al’umma.
You must be logged in to post a comment Login