Labarai
Shugaba Tinubu ya bai wa ‘yan wasa mata da suka lashe kofi kyautar kudi da Gidaje

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bai wa ƴan wasan tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Falcons tukwicin kuɗi har kimanin Dala 100,000 ga kowacce ‘yar wasa.
Haka nan ya bai wa kowa daga cikinsu kyautar gida mai ɗaki uku, yayin da ya bai wa tawagar masu horas da su kyautar dala 50,000.
Shugaban kasa Tinubu, ya sanar da hakan ne a daren Litinin din makon nan lokacin da ya tarbi tawagar yan wasa matan bayan nasarar da suka samu ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na Afirka karo na 10.
Baya ga kyautar kuɗi da gida, Tinubu ya kuma karrama ƴan wasan da lambar girmamawa ta ƙasa ta OON.
A nata bangaren, ita ma kungiyar gwamnonin Najeriya ta bai wa tawagar ta Super Falcons kyautar kudi naira miliyan 10.
You must be logged in to post a comment Login