Connect with us

Labaran Wasanni

U-20 AFCON: Ghana ta bai wa kowa ne dan wasa kyautar dala dubu 10

Published

on

Shugaban kasar Ghana Nana Addo, ya ce, zai baiwa kowane dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar ‘yan kasa da shekara 20 kyautar dala dubu 10 sakamakon nasarar lashe kofin Afirka.

Nana Addo ya yi wannan alkawarin ne a ranar Talata 9 ga watan Maris a wata ziyara da ‘yan wasan suka kai masa bayan dawowarsu daga kasar Mauritania inda suka buga wasan.

Shugaban ya kuma ce za a raba kudin kashi biyu inda kowa zai karbi kashi guda yayin da kuma za a saka hannun jari na tsawon shekaru 10 da kashi dayan.

Ghana dai ta lashe kofin ne bayan da ta doke Uganda da ci biyu da nema a wasan karshe na gasar cin kofin na Afirka na ‘yan kasa da shekara 20.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!