Labarai
Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnoni su fifita walwalar mutanen da suke jagoranta

Shugaban kasa Bola Tinubu ya buƙaci gwamnoni da su fifita walwalar mutanan da suke shugabanta musamman na yankunan Karkara, ta hanyar bunƙasa wutar lantarki da ayyukan noma domin kawar da talauci.
Kiran na zuwa ne bayan gabatar da wani shirin gwamnati na musamman kan bunƙasa tattalin arziki a matakin mazaɓu da aka yi wa laƙabi da ‘Renewed Hope Ward Development Programme wanda ministan kasafi da tsare-tsare ya gabatar a taron majalisar tattalin arzikin ƙasa.
Manufar sabon shirin shi ne tabbatar da bunƙasar tattalin arziki ta hanyar taimaka wa mazaɓun ƙasar nan dubu 8,809 a faɗin jihohi 36, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin ƙasar nan da su yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa rayukan ƴan ƙasar daga tushe.
You must be logged in to post a comment Login