Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya kafa asusun tallafi ga sojojin da suka jikkata da wanda suka rasu a bakin aiki

Published

on

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kafa sabon asusun tallafi na musamman domin taimaka wa sojojin Najeriya  musamman waɗanda suka jikkata a bakin aiki da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, yayin bikin cikar sa shekaru 74, inda ya ce hakan wata hanya ce ta girmama sadaukarwa da jarumtar jami’an soji.

Ya kuma umarci Akanta Janar na Tarayya da ya buɗe asusu na musamman domin gudanar da wannan shiri, 

Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin bayar da duk albashinsa tun daga lokacin da ya hau mulki a matsayin tushen fara wannan asusu.

Ya kuma yi kira ga gwamnoni, ‘yan majalisar dokoki, kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu hannu da shuni da su mara wa shirin baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!