Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan gillar Filato

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa mutane da dama a Kauyen Barikin Ladi da ke jihar Filato tare da bayar da umarnin gaggawa ga hukumomin tsaro dasu kamo wadanda ake zargi da laifin.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasan kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a Talatar makon nan.

Ta cikin sanarwar, Bola Tinubu ya kuma bar da umarnin kai wa al’ummar yankin kayan Agajin gaggawa musamman ga wadanda lamarin ya rutsa da su kwance a asibitoci.

Haka kuma Bola Ahmad Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar ta Filato tare da shan alwashin cewa wadanda suka aikata wannan laifi ba za su kubuta ba, har sai sun fuskanci hukunci akan abunda suka aikata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!