Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin bincike kan rikici APC a Bauchi

Published

on

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya kafa kwamiti karkashin shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, domin kawo ƙarshen rikicin cikin gida a  jam’iyyar APC a jihar Bauchi.

 

A cewar sanarwar da mai bai wa shugaban majalisar shawara kan harkokin yada labarai, Musa Krishi, ya fitar ranar Lahadi, ta ce, Kwamitin zai binciki asalin rikicin wanda ya aka fara tun zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC na kakar 2015.

 

Haka kuma Kwamitin zai gana da jiga-jigan jam’iyyar na jihar ta Bauchi.

 

Mambobin kwamitin sun haɗa da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, sai tsohon shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin Majalisar Dattawa Abdullahi Abubakar Gumel, sai mai bai wa shugaban ƙasa shawara a harkokin siyasa Alhaji Ibrahim Masari, da kuma Alhaji Usman Abubakar Gotomo.

 

Yayin da aka nada Shugaban ma’aikata na ofishin shugaban Majalisar Wakilai Farfesa Jake Dan-Azumi, a matsayin  sakataren kwamitin.

Haka kuma an bai wa Kwamitin wa’adin gabatar da rahotonsa cikin makonni masu zuwa domin daukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!