Labarai
Shugaba Tinubu ya sake aika wa majalisar dokokin buƙatar ƙara ciyo bashin Dala miliyan 347

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake miƙa wa majalisar dokoki buƙatar ƙara ciyo bashi na Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashi na gwamnatin tarayyar na shekarun 2025 zuwa 2026.
Buƙatar na zuwa ne cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na jiya Laraba.
Tinubu ya ce ciyo bashin ya zama dole saboda buƙatar ƙarin kuɗi da aka yi a aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, wanda ya tashi daga Dala miliyan 700 zuwa Dala miliyan 747, ƙarin Dala miliyan 47.
Ko a ranar Talatar makon nan sai da majalisar datttawa ta amincewa shugaba Tinubu ciyo bashin Dala biliyan 21 daga ƙetare.
You must be logged in to post a comment Login