Labarai
Shugaba Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro tare da naɗa wasu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ya sauke babban hafsan Soja Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron a wani sauyi a tsarin jagorancin sojin Najeriya domin ingantawa tare da da ƙarfafa sha’anin tsaro.
Ta cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar mai ɗauke da sa hannun ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban a harkar yaɗa labarai, Sunday Dare, Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.
BBC ta ruwaito cewa, Sababbin hafsoshin da shugaban ya naɗa sun haɗa da:
1. Janar Olufemi Oluyede – Hafsan hafsoshi
2. Manjo Janar W Sha’aibu – Hafsan sojojin ƙasa
3. Air Vice Marshall S.K Aneke – Hafsan sojin Sama.
4. Rear Admiral I. Abbas – Hafsan sojin ruwa
5. Manjo Janar E.A.P Undiendeye – Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.
You must be logged in to post a comment Login