Labarai
Shugaba Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan gillar da aka yi a unguwar Dorayi

Shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu yayi kakkasur suka kan kisan gillar da aka yiwa wata matar aure mai suna Fatima Abubakar da yayanta shida a unguwar Dorayi Chiranci a jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar tace shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin munmunan rashin imani da tausayi wanda ya girgiza al’ummar dama kasa baki daya.
Tunubu ya nuna matukar alhini kan wannan munmunan iftila’in tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Shugaban ya kuma yaba wa rundunar yan sanda bisa gaggawar daukar mataki na kama wadanda ake zargi da aikata laifin.
You must be logged in to post a comment Login