Ƙetare
Shugaba Trump ya nada kwamitin zaman lafiya a Gaza

Shugaban Amurka, Donbald Trump ya bayyana sunayen mambobin kwamitin da zai jagoranta, wanda zai tafiyar da zaman lafiyar Gaza.
Daga cikin mambobin kwamitin har da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio da tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair.
Sauran sun haɗa da surukinsa, Jared Kushner da kuma wakilin Trump na musamman a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff da shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga.
Fadar gwamnatin Amurka ta ce akwai aikin musamman da kowane ɗaya daga cikin mambobin kwamitin zai yi, don taimaka wa zaman lafiyar Gaza.
Shugaba Trump ne zai jagoranci kwamitin, yayin da wasu ƙwararrun ƴan Boko za su kula da kwamitin farar hula a Gaza.
You must be logged in to post a comment Login