Labarai
Shugaba Tunubu ya umarci sojoji su guji sanya kansu a harkokin siyasa

Shugaban Kasa Bola Tunubu ya umarci dakarun rundunar soji da su ci gaba da kiyaye dokokin kasa da kundin tsarin mulki ba tare da sanya kansu a cikin siyasa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wajan taron bikin bude taron shekara shekara na hafsan hafsoshin sojin kasar nan dake gudana a Jihar Lagos
Tunubu ya tunatar da sojojin cewa babban abinda yafi mayar da hankali akai shine kare kasa da ‘yan kasar baki daya
Yayin taron, mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima ne ya wakilci Shugaban Kasa Bola Tunubu inda ya bukaci sojojin da su kara kaimi wajen kula da tsaron kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login