Labarai
Shugaban Jam’iyyar APC na Kano Abullahi Abbas ya nemi afuwa kan kalamansa ga al’ummar Fagge

Shugaban jamʼiyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya nemi afuwar alʼummar unguwar Fagge bayan wasu kalamai da ya yi, inda suka kai ƙarar sa kotu.
A wani saƙon murya da lauyan alʼummar Faggen Barr. Abba Hikima Fagge ya wallafa a Facebook, Abdullahi Abbas din ya ce ba a fahimci jawabinsa ba ne.
A cewarsa, yana nufin Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fagge.
A cewar Abbas ba hujjar da zai ci mutuncin Fagge, idan aka yi la’akari da malamai na addini da na siyasa da aminai da abokai da yake da su.
Ya jaddada cewa yana neman afuwar alʼummar Fagge baki ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login