Labarai
Tinubu, ya umarci dakarun rundunar sojin ƙasar nan da su canja salon yaki da ‘yanta’adda a Katsina

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci dakarun rundunar sojin ƙasar nan da su canja salon da suke bi wajen fatattakar ƴan bingida a jihar Katsina ta hanyar yin amfani da na’urori na zamani wajen sanya ido kan matsalar tsaro.
Shugaba Tinubu, bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gwamnan jihar ta Katsina Dikko Radda da wasu shugabannin jihar a fadar mulki ta Villa da ke Abuja.
Tinubu ya kuma jaddada muhimancin magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan, ya na mai cewa, gwamnatinsa za ta ƙara ɗaukar matakan tsaro na cikin gida, ciki har da yiwuwar kafa ƴan sandan jihohi da ƙarfafa masu gadin dazuka.
Haka kuma, ya buƙaci a rika samun rahoton aikin jami’an tsaro kullum daga Katsina.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kuma bayyana cewa, ya zama dole gwamnatinsa ta kare rayukan jama’a da kuma wuraren ibada da kasuwanci.
You must be logged in to post a comment Login