Labarai
Benue : Shugaban majalisar dokokin jihar ya kamu da COVID-19
Kakakin majalisar dokoki ta jihar Benue Titus Uba da ‘Dan sa sun kamu da cutar Korona
Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren yada labarai ga shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Lubem Tiav ya fitar cewa, tuni shugaban majalisar ya killace kan sa.
Shi dai shugaban majalisar dokokin jihar ta Benue na daga cikin mutan 66 da aka yi wa gwajin cutar COVID-19 a ranar Asabar bayan da ya karbi sakamakon gwajin.
Sakamakon gwajin ya nuna cewar shugaban majalisar da ‘Dan shin a dauke da cutar Korona yayin da sauran mutane 64 gwajin ya nuna cewar bas a dauke da cutar.
You must be logged in to post a comment Login