Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Najeriya za su sha mamaki kan zargin Magu – Garba Shehu

Published

on

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Malam Garba Shehu ya ce ‘yan Najeriya za su sha mamaki   ya yin da ake cigaba da bankado bayanai kan zargin cin hanci da ake yi wa dakataccen mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne a tattauanawar sa da gidan talabijin na Channels ta cikin shirin (Sunday Politics).

Har Ila yau Malam Garba Shehu ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan bincike zargin da ake yi wa Ibrahim Magu zai gabatar da rahoton sa akan haka ne ‘yan Najeriya su kwan cikin shiri wajen shan mamakin abun da rahoton ya kunsa.

Kakakin fadar shugaban kasa ya kara da cewar, ana girmama tare da martaba shugaban kasa Muhammadu Buhari a duniya wajen yaki da cin hanci da rashawa a saboda haka ‘yan Najeriya su sani cewa babu wanda ya fi karfin doka.

Labarai masu alaka  : 

Malami ya dakatar da daraktoci 12 a EFCC

Za a janye ‘yan sandan dake aiki a EFCC

Hukumar EFCC ta gano ma’aikatan bogi 1000 a jihar Kwara

Da aka tambayi Malam Garba Shehu kan mamakin da ‘yan Najeriya za su sha kan bayanan da za su fito bayan da kwamitin ya mika rahoton sa, Garba Shehu ya ce, kwamitin da mai shari’a Ayo Salami mai ritaya ke jagoranta, na shedawa shugaban kasa kan cigaban da ake samu kan bayanan da suka samu a zargin da ake yi wa Ibrahim Magu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!