Connect with us

Labarai

Shugaban Tinubu na shirin ciyo bashin fiye da Dala biliyan 21 da naira biliyan 758

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa Majalisar dattawa bukatar neman izinin karɓo bashin kudi kimanin Dalar Amurka biliyan 21 da miliyan 5 daga ƙasashen ketare da kuma naira biliyan 758 a cikin gida.

 

Ana sa ran za a yi amfani da kuɗin ne wajen aiwatar da muhimman ayyuka kamar gyaran hanyoyi da kiwon lafiya da ilimi da samar da ruwan sha da kuma biyan tsoffin ma’aikata haƙƙoƙin su.

 

Majalisar ta tura buƙatar zuwa kwamitinta mai kula da lamuran bashin cikin gida da na waje, wanda ake sa ran zai gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.

 

Haka kuma, shugaban ya buƙaci a ba shi damar cin bashin ƙarin Dala biliyan biyu daga kasuwar cikin gida domin saka jari a wasu sassa masu muhimmanci na tattalin arziƙi wanda shi ma majalisar za ta tura zuwa ga kwamitin basussuka na gida da waje domin yin nazari.

 

A baya, shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisar yana neman amincewa da sabon shirin rancen kuɗi na shekarar 2025 zuwa 2026.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!