Ƙetare
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya janye barazanar korar jakadun kasashe 10
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya janye barazanar sa na korar wasu jakadun kasashen Turai 10 sakamakon zargin su da matsawa gwamnatin sa lamba.
Musamman na sakin wani dan gwagwarmaya da gwamnatin ta kama.
Tun a Litinin din makon jiya ne Erdogan ya yi barzanar sallamar jakadun kasashen Canada, Denmark, France, Germany, Netherlands Norway Sweden Finland, Newzealnad da Amurka, bisa zargin su da hada baki wajen yi wa kasar zagon kasa.
Duk da cewa ana ganin Erdogan ya yi amai ya lashe kan batun sallamar jakadun, ba kuma tare da ya bada wasu hujjoji ba, ya gargade su da su yi taka tsan-tsan.
Kafin Erdogan ya bada sanarwar sai da majalisar zartaswar kasar ta tattauna batun sallamar jakadun, inda ta ce kai tsaye suna katsalandan ne ga zaman lafiya da kuma tsare-tsaren kasar.
Kasar ta Turkiyya wadda mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO ta jima tana samun rashin jituwa da kasashen turai, saboda banbancin ra’ayi irin na siyasa.
rfi
You must be logged in to post a comment Login