Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugabannin Afurka sun buƙaci raba rigakafin Korona Daidai-wa-daida

Published

on

Shugabannin kasashen Afurka da dama ne suka yi jawabansu a rana ta biyu a taron koli na Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai bayanan shugabannin sun fi maida hankali ne a kan batun coronavirus da batun raba rigakafin annobar daidai tsakanin kasashe.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ya kamata batun tsara rabon rigakafi daidai wa daida a duniya ya zama babban abin da yaki da annobar zai fi maida hankali a kai muddun ana son duniya ta yi nasara a wannan yakin.

Shi ko shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya bayyana yanda annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin Afurka illa, ya ce sama da ‘yan Afurka miliyan 30 ne suka fada cikin tsananin talauci a shekarar 2020.

Kana wasu miliyan 40 kuma ka iya fadawa cikin talauci sakamakon annobar kana ya kwatanta tasirin cutar a kan Afurka da mai matukar muni, inda ya ce ayyukan yi wajen miliyan 100 ne aka yi asarar su.

Ya ce mafita daya ita ce yi wa kimanin kashi 70 cikin 100 na al’ummar Afurka cikin dan lokaci kamar yanda aka yi a wasu wurare; don hakan zai taimaka ainun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!