Labarai
Shugabannin KUST Wudil sun kai wa Sarkin Kano ziyara
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yaba da irin na mijin kokarin da jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil ke yi, wajen inganta harkokin ilimi da nufin samar da dalibai managarta da za su hidimtawa kasa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne a yayin da yake karbar shugabannin Jami’ar ta Wudil karkashin jagorancin shugaban Jami’ar Farfesa Shehu Alhaji Musa a fadarsa.
Sarkin yace jami’ar ta na samar da kwasa-kwasai masu alaka da rayuwar dan Adam ga dalibanta, don su zama shugabanni na gari a kasar nan.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban jami’ar Farfesa Shehu Alhaji Musa, ya ce, sun je fada ne da nufin nuna mubaya’arsu ga sarkin da kuma neman albarka, inda ya bayyanawa sarkin cewa jami’ar ta kirkiro wasu tsangayoyi don bunkasa ilimin jami’ar.
A wani labarin kuma, shugabar kungiyar kula da marayu ta unguwar Fanshekara Hajiya Hadiza Salisu, ya ziyarci fadar sarkin Kano inda ta sanar da sarkin irin hidimomin da suke yi wa al’umma na jinkai da suka shafi marayu da zawarawa da kuma bangaren ilimi.
Wakilinmu na fadar Sarkin Kano, Muhammad Harisu Kofar Nasarawa ya ruwaito cewa, a yayin ziyarar shugabar kungiyar tana tare da manyan jami’an kungiyar maza da mata.
You must be logged in to post a comment Login