Labarai
SIYASA: Jiga-jigan PDP 7 sun ajiye mukamin su

Bakwai daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP na kasa suka ajiye mukamansu nan take.
Shugabannin da ke rike da mukamai daban-dabam sun rubuta takardar ajiye mukaman na su ga shugaban jam’iyyar na kasa, Mista Uche Secondus a daidaikun su.
Sai dai kuma ba a tantance sunayen wadanda suka ajiye mukaman nasu ba, amma ana zargin wadanda suka ajiye mukaman sun kasance mataimaka ne na musamman.
Rahotanni sun bayyana cewa, sakataren tsare-tsare na jam’iyyar, Mista Austin Akobundu ya tabbatar da ajiye mukaman nasu.
You must be logged in to post a comment Login