Labarai
Sojoji sun cafke ƴan bindiga a Katsina
Rundunar soji ta “Operation Sahel Sanity” ta cafke ƴan bindiga 38 a shiyyar arewa maso yammacin kasar nan.
Jami’in jami’in hulda da jama’a na rundunar Kanal Ahmad Iliyasu ne ya bayyana hakan a ofishinsu da ke Faskari, a jihar Katsina.
Ya ce, sun samu wannan nasara ne daga 4 ga watan Satumban da ya gabata, zuwa 25 ga watan Oktoban da mu ke ciki.
Rundunar ta kuma kama mutane 93 da ake zargi da bai wa ƴan ta’adda bayanan sirri.
Sannan sun ceto mutane 108 da aka yi garkuwa da su.
Sun kuma kwato Shanu 131, awaki da tumaki 154 wanda suka mayar da su zuwa ga masu su.
You must be logged in to post a comment Login