Labarai
Sojoji sun daƙile harin ‘yan Boko Haram

Dakarun sojin Najeriya sun daƙile wani hari da ‘yan tada kayar baya na Boko Haram suka kai wani sansanin soji da ke Buni Yadi, a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dakarun sun hallaka ‘yan ta’addan da dama, sai dai an samu asarar rayukan wasu daga cikin jami’an sojin.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa a lokacin da suka samu ƙarin runduna, inda hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa.
Wani soja ya tabbatar da cewa sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da ƙwato motoci biyu da makamai da dama daga hannun su.
Sai dai wani daga cikin mazauna ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce, an samu zaman lafiya bayan faruwar harin.
You must be logged in to post a comment Login