Labarai
Sojoji sun hallaka ƴan ta’addan ISWAP tare da kama mutane 19 da ake zargin shan ƙwayoyi

Dakarun soji, sun hallaka wasu ƴan ta’adda na ISWAP, tare da kama mutane 19 da ake zargin suna tu’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare daban-daban a fadin Najeriya.
Ta cikin wata sanarwar da rundunar soji ta wallafa a shafukan ta na X, da Facebook, ta tabbatar da cewar yayin samamen da ta kai ta yi nasarar kama masu tallafa wa ’yan ta’adda, da shugabannin masu garkuwa da mutane sai ƴan ƙungiyar asiri da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Rundunar ta ce, jihohin da dakarun suka samu wannan nasara sun haɗa da Borno da Adamawa da Zamfara sai Kaduna da Benue da Kwara da Nasarawa da kuma Imo.
Sauran jihohin sun haɗa da Anambra da Delta da Bayelsa da kuma Rivers.
Haka kuma ta ce, Sojojin sun ƙwato bindigogi da harsasai da Bama-bamai sai Babura da man fetur da aka sarrafa ba bisa ƙa’ida ba da kuma tarin miyagun ƙwayoyi.
Rundunar ta ce, a Zamfara da Kaduna, sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kama ƙasurguman shugabannin masu garkuwa da mutane, yayin da a Benue da Kwara aka kuɓutar da fasinjoji da mazauna ƙauyukan da aka sace su a wasu hare-hare daban-daban.
A Kudu maso Kudu kuma, jami’an tsaro sun ƙwato sama da lita 1,200 na man dizal da ɗanyen mai da aka sarrafa ba bisa ƙa’ida ba tare da haɗin gwiwar hukumar NDLEA wajen daƙile hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.
You must be logged in to post a comment Login