Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu Ganduje ya yi wa Abba Kabir Yusuf addu’ar yin mulki cikin nasara

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yiwa sabon zabebben gwamnan jihar mai jiran gado Engr Abba Kabir Yusif, fatan gudanar da mulki yadda ya kamata.

Gwamna Ganduje ya yi masa wannan fata ne lokacin da yake zantawar da manema labarai yau Asabar bayan kammala addu’ar neman zaman lafiya da ci gaban jihar Kano da kuma yi wa shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmad Tunubu, addu’o’in fara mulki cikin nasara a wani bangare na taya shi murnar cika shekaru

saba’in da daya da da haihuwa.

Bayan kammala taron addu’ar a dakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jihar, gwamna Ganduje ya kuma bayyana cikin harshen Turanci cewa, nasarar da Engr Abba Kabir Yusif, ya samu ta wucin gadi ce.

Haka kuma ya kara da cewa za su kalubalanci nasarar tasa a gaban kotu, kuma zai kafa kwamitin mika mulaki cikin salama.

Taron addu’ar ya samu halartar malamai maza da mata da kuma kungiyoyin Tijjaniya da Kadiriya da kuma kungiyar Izala.

 

Rahoton: Abba Isah Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!