Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun kashe ƴan bindiga a Adamawa

Published

on

Jami’an tsaro a garin Maiha na jihar Adamawa sun samu nasarar kashe wasu ‘yan bindiga tare da kwato manyan makaman harba roka guda 11

Mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Maiha kan harkokin yada labarai Abdulganiyyu Pakka ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, inda ya ce sun gano wasu abubuwa masu fashewa guda uku.

Sanarwar ta ce ‘yan bindigar sun je garin ne daga Jihar Zamfara, kuma jami’an tsaron da suka gudanar da aikin samamen sun hada da sojoji da kuma jami’in sintiri na sa kai.

Mai magana da yawun runduna ta 23 da ke Yola Manjo Sani Muhammad ya tabbatar da kai samamen da jami’an suka yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!