Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Sojoji sun kashe ƴan Boko haram 40 a jihar Borno

Published

on

Dakarun Operation Hadin Kai na rundunran sojin ƙasar nan sun hallaka ƴan boko haram da dama a ƙauyen Dawuri da ke yankin ƙaramar hukumar Konduga a jhar Borno.

 

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa sojin na Najeriya sun yi amfani da manƴan bindigogi da makamai masu nisan zango wajen luguden wuta kan ƴan ta’addar na Boko haram waɗanda ke wani taro na tsara yadda za su kai hare-hare a birnin Maiduguri.

 

Wani jami’in soji da ke cikin bataliyar sojojin da suka kai harin, ya shaidawa jaridar ta PRNigeria cewa, sojojin sun kai harin ne biyo bayan samun wasu bayanan sirri.

 

A cewar sa, yayin harin sojojin sun kashe ƴan ta’addar na boko haram guda arba’in,yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!